Description

A wani zamani mai tsawo da ya shuɗe, an yi wani babban Sarki ana kiransa Shamsuddini. Ya kasance mai girman iko. Mulkinsa ya watsu cikin ƙasashen duniya, tun daga Kurasana har zuwa Sistani har iyakar tekun hindu. Babban birninsa shi ne Kunaimu Madudu. Yana da Wazirai goma waɗanda ke mulkin wasu jihohin daga ƙasarsa. Ƙarƙashin kowane Waziri akwai hakimai dubu, da dagatai dubu goma, da sauran masu faɗa a ji. Yana da mayaƙa, da bayi, da hadimai, da dukiya mai ɗumbin yawa. Talakawa na sonsa saboda yawan adalcinsa da kyautayinsa gare su. Sai dai duk wannan abubuwa da ya tara ba shi da mata. Ya taɓa yin auren bai ji daɗi ba, don haka ya jinkirta har ya samu wadda za ta yi masa biyayya sau da ƙafa.

Wata rana ya shirya tare da bayinsa suka fita farauta. Yayin da suka gama zagaya daji suka kamo hanyar gida sai suka yi kiciɓis da wani baƙin bawa yana haye bisa alfadara, biye da shi wata taguwa ce ɗauke da darbuka na zinariya yana ta ɗaukar ido. Sannan biye su mayaƙa ne cikin shiri, suna haye kan dawakai, gaba da su wasu dawakan ne ɗauke da jauhari da lu’ulu’u, suna tafiya cikin tsari. Da Sarki Shamsuddini ya gan su sai ya zabura bisa dokinsa, ya isa wajen bawan nan ya ce masa, “wannan matar ina za a kai ta?” Shi bawan bai san Sarki ba ne, sai ya ce, “wannan ‘yar Waziri Yusuf ce, za mu kai wa Sarki Imranu ya aure ta.”

A daidai lokacin da suke magana sai ‘yar Waziri ta leƙo da kanta domin ta ji an tsaya da tafiya, sai kuwa Sarki Shamsuddini ya yi ido huɗu da ita. Ya yi duba izuwa ga ƙirar jikinta, da fararen idanunta, da kyawawan leɓɓanta, nan da nan ya ji son ta ya shige shi. Ashe ita ma yayin da ta yi duba zuwa ga Sarki sai ta ji tana son sa.

Sarki ya ce da bakin bawan nan, “ka sani Waziri Isfahanu a ƙarƙashin mulkina yake. Ni ne Sarki Shamsuddin, ina son wannan yarinyar, don haka ka ba ni ita na aure ta.”

Bawa ya ce, “ai ni ɗan aike ne, ba zan aikata abin da ubangidana bai umarce ni ba.” Sarki ya fusata ya ce, “Kai ɗin banza kai ɗin wofi! Ko shi Wazirin da yake bawan bawanmu bai isa ina son abu ya ki amincewa ba!” Ya daka wa bayinsa tsawa suka kama akalar alfadarar nan suka wuce da ita gidansa. Mayakan nan na ganin haka sai suka juya tare da bakin bawa suka koma wajen Waziri Isfahanu suka shaida masa abin da ya faru. Waziri na jin haka ya fusata matuƙar fusata, ya kawo iyakar wuya. Ya ce, “wannan mugun Sarkin ya bautar da ni, yana son bautar da iyalina ma. Ku sani ban ba shi wannan ‘yar ba, kuma ba zan yarda ya taɓa ta ba. Idan kuwa ya aikata hakan to a bakin ransa.”

Duk da ya faɗi haka sai ya aika da takarda zuwa ga Sarki yana mai cewa, “ka sani ni bawanka ne ɗan bayinka. Kenan ‘yata ma mallakinka ce, sai abin da ka ga dama da ita? Akan haka ba ni da ta cewa.” Da Sarki ya ga wannan takarda sai ya cika da murna da farin ciki, ya sa aka shirya walima mai yawa. Ya aika wa Waziri kyautar bajinta, aka shiga hidimar aure da shagulgula. Bayan an ƙare shagali, Sarki ya shiga wajen matarsa ya tare da ita, babu jimawa ta samu ciki.

Waziri kuwa sai ya riƙa aika wa ragowar waziran wasiƙa a ɓoye yana shaida musu irin abin da Sarki ya yi masa na tozarci. Dama ashe duk suna jin haushin sa. Nan da nan suka taru a wajen Waziri Isfahanu suka shirya yadda za su kashe Sarki kowa ya huta. Bayan sun kare shiri kaf suka durfafi babban birnin ƙasar, duk abin da ake ciki Sarki ba shi da labari. Yana ɗakin matarsa suna cin amarci sai suka ji hayaniyar dawaki, da ihun mazaje, da karar mata da yara.

Sarki ya dubi matarsa wadda ke da tsohon ciki ya ce mata, “wace dabara za mu yi?” Ta ce, “kai ke da gani duk abin da ka gani shi za mu aiwatar.” Ya ce, “babu sauran zama a nan, mu tsere da ranmu.” Suka tashi suka shirya dawakai biyu, sannan suka ɗauki jakankunan kuɗi masu yawa suka bi ta bayan gida suka gudu su biyu kaɗai. Cikin duhun dare suka yi ta tafiya cikin ƙungurmin daji basu san inda suke tafiya ba.

A wannan daren naƙuda ta kama matar saboda wahala da fargabar da ta shiga. Nan ta durƙusa ta haifi ɗa namiji. Sarki Shamsuddini da kansa ya yi mata hidima, babu ruwa, sai tufafi suka sa tsumma suka goge shi sannan ta soma shayar da shi. Suka samu wani kogo suka ɓuya a ciki bayan sun ɗaure dawakansu a wuri mai nisa yadda babu wanda zai gan su….

You cannot copy content of this page