Description

Cikin daren nan ban runtsa ba. Idona biyu har aka yi assalatu. Duk sa’adda na yi juyi sai na ji wani irin dunƙule kamar curin fura ya taso daga tumburƙuma ta ya tokare kafofin shaƙar numfashi na. Sai na ji na rasa walwala ina tuna irin cin zarafin da tsamurmurin mutumin nan ya yi min. A ganina ko da baƙaƙen maganganun da ya farfaɗa min sun isa su fusata ni. Maganganun suka riƙa diro min kamar dirar harsashi kamar ta amsa kuwwa.

“Ɗan tsuguni da kai. Yaushe ka isa aure? An gaya maka aure abin wasa ne ko ƙiriniya? Wacce sana’a gare ka? Mene ne matsayin iliminka? Kada ka ƙara zuwa gidan nan idan kana son kiyaye mutuncinka, kodayake ba ka san shi ba da tuni ka daina damunmu da zuwa wajen ‘yarmu da sunan zance ba tunda aniyarka ba ta alheri ba ce. Mutumin kawai!”

Maganganun suka yi ta dawurwura a ƙwaƙwalwa ta kamar amsa kuwwa.

Na yarda ban isa aure ba saboda ban mallaki ko daya daga sharaɗan da aka gindaya na yin aure ba. In ban da shekarun munzali ban mallaki wani abu ba daga sharuɗɗan da suka gindaya min. Karewar ta ma, ‘yar sana’ar da nake yi ta rini an rushe rumfar kan cewa ta hau kan titi. Yanzu dai bani da aikin fari balle na baƙi, ina kuwa zan samu tsububin kuɗi har dubu ɗari da sunan kuɗin gaisuwar aure? Da na mallaki wannan adadin ma ai ba zan kashe su haka ziƙau ba, sai na ware waɗanda zan ɗinka sutura ta kece raini, hakan zai sa ƙila na huta da gorin tsohon nan wai shi kakanta, idan zai kore ni yayin da na je gidansa zance.

“Kana yawo da riga kamar ta ƙaninka wa zai ba ka auren ɗiyarsa? Tafi ka koyi saka suturar kirki. Kar na ƙara ganinka ƙofar gidana.” Ya sha maimaita min wannan maganar. Ni kuwa da naci kamar makahon kare, ba na iya daurewa sai na je na yi ido huɗu da sahibata Bahijja. Danginta duka sun nuna a zahiri ba sa tare da ni. Yau dai ta faru ta ƙare, an yi wa mai dami ɗaya sata….

You cannot copy content of this page